LADUBBA GUDA 11 NA TILAWAR ALQUR'ANI

LADUBBA GUDA 11 NA TILAWAR ALQUR'ANI
LADUBBA GUDA 11 NA TILAWAR ALQUR'ANI

Babu wani abu da yafi chanchantar a bashi ladabi da kyautatawa lokacin yinsa kamar Maganar Ta'ala wato Alqur'ani mai girma.

Alqur'ani mai girma yana buqatar Ladubban da kyautatawa ta musamman lokacin karantasa da Tilawarsa da lokacin kokarin sanin ma'anoninsa.


An tambayi babbar Majalissar bada fatawa ta kasar Saudiyya mai suna:
""اللّجنة الدائمة للإفتاء برئاسة الشَّــيخُ العلّامــة/ عـبدُ الـعَزِيـز بن بـاز -رحمهُ الله":-
TAMBAYA
"Wadan nene manyan Ladubban tilawar Alqurani mai girma??".

AMSA:
Tilawar Alqurani mai girma tana da ladubba masu yawa,ga kadan daga cikinsu;-
1-Mai Tilawar alqurani ya zama mai kyakkyawar Niyya da ikhlasy acikin karatunsa da neman yarda fuskar Allah da wannan tilawa tasa da nisantar dukkan wata Riya da Sum'a da neman dukiya ko neman ladar duniya da abin duniya da tilawarsa ta littafin Allah,ya zama yayi karatunsa ne da tilawarsa dan Allah shi kadai,dan neman kusanci zuwa gare sa shi kadai.

2-Ya fara karatun alqur'ani da neman tsarin Allah daga shaidhan,sannan ya fadi:
بـسم الله الـرحمن الـرحيم.
Idan zai fara karatun sa ne daga farkon sura,in banda farkon Suratul Tauba,itace wadda ba'a karata-
بـسم الله الـرحمن الـرحيم
Lokacin da za'a fara karanta ta daga farko.

3-An so mai karanta alqurani ya zama cikin alwala,idan zaiyi karatun ne daga littafin alquranin,to anan wajibine yayi alwala, awajan mafi yawan malamai magabata,saboda fadin Manzon Allah ﷺ :
(Babu mai taba alqurani sai mai tsarki).

4-An so ya zauna lokacin tilawar alqurani a kyakkyawan yanayi, yana mai sanya tufafai mafi kyau, yana mai fuskantar alqibla,kuma yayi tilawar a wajan da baza'a tozarta alqurani ba.

5-Yana mai Tawali'u da nutsuwar zuciya da gabbai,lokacin tilawar alqurani,tare da yin tunani ga abinda kake karantawa na ayoyin Allah,tare da girmama maganar Allah.

Kada ka yanke ayar alqurani dan yin magana da wani,sai dai ka ida ayar sannan kayi maganar idan ta kama dole.

6-Ya karanta alqurani dalla-dalla daki daki tare da baima kowani harafi hakkinsa lokacin karatu,domin kana karanta maganar Allah ce,ba maganar waninsa ba,tare da kiyaye Hukunce hukuncen Tajweedi gwargwadon iyawarka.

7-Idan wani yana karatun alqurani a kusa da kai,ko wani yana sallah,to ka sassauta sautinka dan kada ka rikitasa wajan karatunsa.

8-Kada yariqa karatun cikin sauri yadda zai kasance baima sannan me yake karantawa ba, ko yariqa yin jà mai yawa har ya riqa kara wani harafi wanda baya cikin littafin Allah,Kariqa yin karatu matsakaici.

9-Kada ya riqa karanta alqurani da waken kida,kamar yadda Kirista sukeyi a chochi,ko da wani irin yanayi da sigar da tasabawa karatun magabata.

10-Yana cikin manyan ladabin karatun alqurani,mutum ya tsaya da karatu idan hamma tazo alhalin yana tilawa,sannan sai yaci gaba idan ya gama hammar,dan girmama maganar Allah,domin hamma daga shaidhan take.

11-Yana cikin Manyan ladabin tilawar Alqurani ka tsaya a wajan Ayar datake bayani akan Rahama,sai karoki Allah rahama,idan kazo wajan ayar da rake magana akan azaba da fishin Allah sai ka roki Allah ya kareka daga fadawa cikinsu,idan anzo wajan Tasbihi kayi tashihi koda acikin sallah ne,amma banda sallar Farillah.

Idan kuma kazo wajan sujada kayi sujada koda kana cikin sallar farillane.
-الفتوى رقم ( ١٨٦٧٦ ) ] .


Allah ne mafi sani


Post a Comment

0 Comments