LITTAFI: DR. AHMAD💗

DR. AHMAD💗

             1
 
NA MAMAN KHADIJA


    Kusan a jiga ce ya shigo gidan idanun shi duk sunyi ja sabida masifar tafiyar daya shawo fatan shi kawai ya jishi yana watsama jikin shi ruwan sanyi, "Assalamu alaikum." ya furta cikin siririyar muryarshi.

"Wa'alaikumussala na Maman shi ka dawo kenan, sannu da zuwa kawo jakar in ta yaka d'auka kaji Allah yayi maka albarka insha Allahu wataran za kayi alfahari da wannan wahalar da kake sha kaji?"

Cikin jin dad'i ya mika mata jakar littatafan sannan ya d'auki bokitin ruwan dake cike wanda dama ya san nashine kullum ya kan dawo ya tadda ruwan wankan shi Mama ta zuba ta ajiye mai. Ya jima yana wankan sannan ya fito kallon d'aya zakai mishi kasan cewa yanzu ya dawo hayyacin shi ba kamar d'azu daya shigo ba.

Saida ya shiga d'akin shi ya gama shirin shi sannan ya nufi d'akin mahaifiyar tashi cikin shi nata kukan yinwa. gaida ta yayi sannan ya amshi samirar da take miko mishi ya faracin shinkafa damai da yajin dake cikinta, kamin yace

"Mama ina aminu yayine naji banji motsin shi ba?"

Tace "iko yanzu khadija tazo nemanshi wai Maman ta zata aike shi."

"Babana ya karatun naka ina fatan lafiya lau ko?"

"Alhamdulillah wallahi mun kusa shiga aji shidda ai ni sonake kawai inganni cikin jami'a Mama."

"karka damu na Maman shi insha Allah kamar yaune kai-dai kaci gaba da maida hankali domin zaka zama duk abinda kakeso a rayuwa idan har ka dage."

"Mama bari in d'an kwanta kamin la'asar saina leka wajan d'inkin."

gadon shi ya haye wanda yaci gadon shi bayan mituwar mahaifinshi babu wata katifar kirki ammafa yaji gyara domin saika rantse ba kwana akeyi kanshi ba. tabbas bacci yaso yayi idanunshi cike suke da bacci da gajiya saida yana hawo godon yajishi cikin wata irin matsananciyar bukatar mace, nan da nan ya fara juye- juye jikin shi yai wani iri cikin kasala ya tashi ya koma kan dardumar shi dake k'asa shimfid'e ya kwanta tare da dukunkune jikin shi waje d'aya. Tun yana jin wani mugun sanyi har ya samu da temakon addu'o,in da ya keyi wani barci yayi gaba dashi.


Saida ya kuma watsa ruwa sannan yafice masallaci bayan ya gayawa Maman shi cewa zai wuce wajan d'inki daga masallaci domin Ahmad ya kan yi d'in kuna awani shagon abokinshi dake cikin unguwar aduk lokacin da ya dawo makarantar boko.


********

   "Kai babana idan ka gama sharar ka bar wanke bayin nayi idan nagama abinda na keyi kajiko? kai maza kazo ka karya ka tafi kadda ka makara kasan dai tafiyar dake gabanka ko?"

"Mama ki bari na gama miki kuma ni azumi na keyi yau, kai Aminu zoka amshi kud'in tara ka wuce."

kusan da mamaki take kallonshi bayan ta isa gaban shi tace "kai babana bani son sakarci yau yaushe?"

Sadda kanshi k'asa yayi kamin yace "Mama yau laraba."
"To me yasa ka tashi da azumi yau tunda kasan alhamis da litinin kawai na amince kayi azumi iye?" kiyi hakuri Mama bawai nasab'a umarninki hakan nanba wallahi ba haka bane kawa gani nayi azumin shine mafita agareni shi yasa na tashi dashi amma kiyi hakuri bazan Kara ba."

Jinjina kanta tayi sannan tabar wajan zuciyarta cike da tausayin yaron nata ammadai ta d'auki alwashin jin damuwarshi yau idan ya dawo daga makaranta domin ba taso wata lalura ta kamashi.

Cikin biyayya ya duka ya amshi kud'in kamin yace "yayana nagode Allah yasaka maka da Alkhairi kuma jiya aunty khadija tace tana gaida ka."  cewar Aminu kanin Ahmad wanda ke sanye da kayan primary na gwamnati.

murmushi Ahmad d'in yayi kamin yace to madallah ina amsawa kai maza katafi kaji ko banda wasa me kakeso in siyo maka idan zan dawo? "Aminu ya washe gibin dake bakin shi daya ke yafara famfara kamin yace "yaya alawa me tsinke."

Dariya Ahmad d'in yayi kamin yace "to wawulo sai naga idan kayi karatu sosai sannan nikuma zanyo maka tsaraba."

"Babana baza kazo ka tafi ba ka biye ma Aminu da surutin shi ko?"   cewar Mama daga cikin d'akin ta domin tana jin duk maganar da su keyi.


*****

 Lafiya lau yaje ya dawo babu wani damuwa cikin ranshi fatanshi arayuwa be wuce yaga ya zama wani abuba kodan dangin mahaifinshi wa inda kullun burunsu be wuce ganinshi awukance ba.

Suna zaune suna tattauna halin rayuwa bayan gama cin abincin su na dare yayin da Aminu tuni ya bingire ajikin Ahmad d'in yana barcinshi sabida shi indai cikin shi ya cika to babu abinda ke biyo baya sai bacci.

cikin nutsuwa ta kalleshi kamin tace "babana ina son kabani duk nutsuwarka anan yanzu sabida bani son ka boyemin damuwarka domin duk duniya baka da kamata kanaji ko? sabida haka ka gayamin banda karatu menene damuwarka??"

marairaicewa yayi kamin ya kalleta sai kuma ya kuma sadda kanshi k'asa yana wasa da dogon hancin aminu wanda keta bacci abinshi.

"Ina jinka babana
a hankali kamar me rad'a ya furta kiyi hakuri Mama wallahi aure nake bukata wallahi nayi bakin kokarin ya kice tunanin araina kodan karatuna sannan ba wani karfine da muba amma na kasa shi yasa nake ya waita yin azumin.....



     Wata irin zufa ce taji ta fara karyo mata lokaci guda tunanin mahaifin shine ya taso mata idanunta ta zuba mishi tana karantar duk wani yanayin daya ke ciki kamin ta sauke ajiyar zuciya tace,

"Babana tun yaushe kake son auren?"

kanshi a k'asa yace "tun shekaru biyu da suka wuce Mama na rasa yadda zanyi dan Allah Mama ki temakeni."

Lissafin shekarunshi ta fara yi inda lissafinta ya nunamata yanzu yana shekara ta cikin goma shabakwai.
   
"To tashi kaje ka kwantar dashi kaima sai ka kwanta da safe za muyi magana."

A sanyaye ya kai Aminu kan shimfid'arshi kamin ya bar d'akin yana cike da tausayin mahaifiyar tashi dan yasan ba k'aramin tashin hankali yasa ta ba.

kusan kwana yayi yana gayama Allah damuwar shi duk da cewa shi Allah masani ne abisa dukkan komai na fili dana b'oye, amma yana so ka kwantar da kanka gareshi ka kai kukanka gareshi bawai dan be san halin da kake ciki ba. yaso ya kuma tashi da azumi sai dai sam baya san damuwar Maman tashi domin ita gani ta keyi kamar cutar yunwa zata iya kamashi.

kanshi a k'asa yake gaidata bayan dawowarshi masallaci kamin yace "Mama me zan dora yanzun?" d'an murmushi tayi  kamin tace "ah'ah babana so nake zaka huta yau."

Murushi kawai yayi har lokacin be kalleta ba domin samun kanshi yayi da wata irin kunyarta, jin yayi shiru ya sata cewa "taliyar murje zaka dafa mana yau saika zabi kalar wacce kakeso ta manja kota mangyad'a kayi mana akwai komai na bukata na ajiye cikin kitchen."

Gidan ya fara gyarawa kamar yadda ya saba kamin ya d'ora  girkin yana yi yana bin sautin karatun Alqur'ani a cikin wayarshi k'aramar nokia a gidan wani Redio da akasan ya.

Yana ta zullumin zatai mishi magana sai yaga sab'anin hakan domin har yayi mata sallamar tafiya makaranta beji tace mai komai ba.


Bayan tafiyar su makarnta ne ya sata d'ora tuwon masara wanda ta juyeshi cikin kulla sannan miyar ma haka, shiri tayi cikin riga da zani na atamfa da dogon hijabinta sannan ta rufe gidan ta nufi gidan aminiyarta kuma matar aminin mahaifin su Ahmad gida hudune kawai tsakanin su.
     
Murna kamar zasu cinye junansu kai kace watanni suka d'auka basu had'u ba. Bayan sun gaisane Maman Ahmad tace "uhum Maman khadija nifa tafe nake da magana bakina Allah yasa malam yana nan yanzu?"

Maman khadija tace "aiko yana nan sabida yanzu ya dawo daga gidan gaisuwar malam iliya, wanka ya keyi yanzu Allah yasa dai lafiya?"

 Mama khadija ta tambaya cikin jimami "To bari dai malam d'in yazo kyaji yaron kun wallahi ke son d'auko min magana..!!!"

Saida malam Mamuda ya gama shirin shi cikin d'akin shi sannnan ya taddasu sunata hirarsu. Bayan sungaisa ne yake tambayarta lafiya ko Maman Ahmad?

Tace "Eh to malam dama akan babana ne."

 Malam Mamuda ya gyara tsayuwa tare da cewa "To to naji dai ina jinki ainasan Ahmad beda wata illa arayuwa kuma insha Allah bamafatan yasa meta nan gaba meya faru dashi d'in?

 Tayi shiru ita kanta maganar nauyi take mata tajima cikin yin shiru sannan tace "Tun watan nin baya naga ya dage da yin azumi kusan kullun  to shine naimishi fad'a sosai sabida ina gudun kadda cutar yunwa ta kamashi (olsa) toh kuma dai be dena ba tun yana yi alhamis da litini duk sati sai naga yanzu duk sanda yaga dama yi yake, to jiya na turke shi da tambaya shine yace min wai bukatar aure ke damunshi to nikuma naga babana duka nawa yake da zai san wannan abin shine nace bari nazo naimaka magana ko zaka ganar dashi ya bari sai nan gaba  karya ja mana surutun mutane."

Malam Mamuda ya ajiye asuwakin shi gefe kamin yace "ikon Allah to Alhamdulillahi tabbas wannan lamari dole mugode ma Allah domin Ahmad yana da nutsuwa sosai kuma tunda ya nuna yana so to insha Allah baza mu tauyeshi ba domin gashi yana da kokarin ganin ya kare kanshi daga sab'awa Allah ta hanyar yin azumi, dan haka dole mu samami shi mafita tun kamin abun yafi karfin shi a zo ana da ansa ni."

"Maganar karatu kuma wannan babu abinda zai gagara insha Allah zai kai duk matakin da ya keso ya kai."  cikin farin ciki Maman khadija tace "kin ga shike nan sai mu aura mishi kanwarshi khadija hankalin mu kwance ko malam?"

Shima cikin farin ciki yace "Nima tinanin da nayi kenan sabida haka gobe kije ki shaidama dangin mahaifin shi sabida afita hakkinsu sannan ki shaida mishi cewa yazo su gaisa da kanwar tashi Allah yayi mana jagoranci cikin lamarin."

Tsabar farin ciki yasa Maman Ahmad sakar musu kuka domin tabbas wa innan mutane sun cika mutane sannan kuma sun rike amanar zumunci da sanin hakkin makotaka.
Da kyar suka lallashe ta sannan tayi musu sallama.
sai kuma zullumin yanda dangin mijin nata zasu amsheta idan ta je musu da zancen. A hanya ta had'u da khadija tun daga nesa take karema yarinyar kallo lokaci guda ta kalli kirjinta babu komai na daga dukiyar kirjin kai daka ganta kasan yarinya ce sharaf innalillahi ta furta kamin ta kauda tunaninta akan abun tana amsa gaisuwarta tace "Mama zanzo na tayaki hira yau tun da babu islamiyya."

Cikin jin dad'i Maman tace "To d'iya ta dama gashi yau mutuminki nayi da ranarnan tuwo sai kinzo sai kici ki koshi."

"To mama sai nazo wanka da salla kawai zanyo in taho gidan ki......"


   Da sallama  ta shiga gidan nata sannan ta d'auki buta bayan ta rataye hijabinta akan kyauren kofarta har yanzu mamakin irin k'irkin mutanen take yi tabbas sun jima suna yi mata halacci tana fatan itama Allah ya bata ikon ganin ta kyautata musu kamar yadda suma koda yashe burunsu suga hankalin ta ya kwanta.

Ta jima cikin sujjadarta ta karshe da kyawawan adduo'i ga mijinta da iyayenta sannan ya ranta guda biyu kacal wanda Allah ya azurtata dasu. Tun kamin ta gama lazumin da ta keyi Aminu yayi sallama hankalin shi nakan kulolin abincin dake ajiye kowa dai ya san yanda ake dawowa makaranta da yunwa da kyar ya zare takalman sandal d'in dake kafafunshi ya zauna sai kallon Maman tashi yake da alama jira yake kawai yaga ta mike ko tayi mai nuni tace ya d'auka.

"Mama ki tashi ki zuba min yunwa zata kasheni." dariya tayi kamin tace "Toh rago kai kam Aminu baka wasa da cikinka ba kamar yayan kaba kaje ka wanko hannu kamin nan na zuba maka."

Yanaci tana kallon shi sosai take ganin kamar da yayi da ita bakamar Ahmad ba wanda yake kallo d'aya zakai mishi ka gane agwai ne.
   
Sai wajan biyu da rabi sannan ahmad ya shigo gidan kai tsaye d'akin shi ya shige sai da ya kwale kayan jikin shi sannan ya nufi d'akin Maman, "Mama sannu da gida na dawo."

"Yauwa babana sannu da dawowa ga ruwan wankan ka can ka farayi saika zo kaci abinci."

Saida yayo wankan ya kintsa sannan ya nufi d'akin nan ya tadda Aminu zaune yana kallon tv. Gaishe ta yayi sannan ya zauna shima yaci tuwon hankalin shi kwance lokaci zuwa lokaci yana kallon Maman tashi sabida yaga sai murmushi ta keyi.

"Mama ki gaya min mana ta samu ne naga kina tayi min murmushi?"
dariya tayi kamin tace "kawai dai ina cikin nishad'i ne sabida yarona zai ajiye iyali."

Kusan da gudu yabar d'akin yana dariya kamin ta bud'e miryarta itama tace "kaje babanku na kira idan ka huta...!!"

Saida yaji anfara kiran sallar la'asar sannan ya tashi kayan ya saka sannan ya fito waje dan d'aura alwala.
Da khadija ya fara cin karo cikin doguwar riga ta material tayi kyau sosai tayi acuci da gashinta Aminu take yan kema farcen shi sabida ta fishi wayo da dabara tana ganin shi tace.

"Lhha ya Ahmad sannu da tashi tun d'azu nazo Mama tace bacci kake yi ina yini?"

Murmushi yayi kamin ya amsa da "lafiya lau ya makaranta?" Murmushi kawai tayi wucewa yayi yana mamakin rashin maganarta wani lokacin yana k'okarin fita yace.

"kuce ma Mama na fita masallaci Aminu naga ta fara sallah."

A dawo lafiya su kayi mishi sannan ya fice.

A masallaci suka had'u da malam Mamuda ganin irin kallon da yake bin shi da shi ne ya sashi jikin shi yin mugun sanyi domin yana jin mutumin kamar mahaifinshi tabbas idan be yarda da bukatarshi ta aureba to zai hakura yaci gaba da danne abinda ke taso mishi.

Hannun Ahmad malam Mamuda ya rike a haka har sai da suka je gidan shi sannan ya tsayar dashi a zaure. Lokacin jikin shi harya fara rawa sabida be san me zai faruba.

"Ka kwantar da hankalinka Ahmad insha Allah zan tsayamaka akan duk abunda kake so matukar be sab'ama shari'aba d'azu  Mamanka tazo min da sakonka shine nace me zai hana ku dai-daita da kanwarka duk da dai tayi kan kanta da yawa ammadai nasan zata iya ragemaka wani abun sannan kuma kaga kaima kayi yarinta da yawa yanzu duk gun wanda naje nemamaka auren abin ma surutu zai zama koba haka ba?"

Cikin wani mugun jin nauyi jikin shi na rawa zuciyar shi na bugawa yace "haka ne baba." Malam Mamuda ya gyra tsayuwa kamin ya fara yi mai nasiha sosai, Ahmad ya d'ora dayi mishi godiya kamar bakin shi zai sakko k'asa.

"kadda ka damu Ahmad ni mahaifinka ne zan yi komai dan farin cikinka, yanzu zaka iya hakuri har karshen shekara kokuwa kana ganin a d'aura auren alabashi daga baya idan angama gyaran inda zaku zauna sai kawai ku tare?"

Shi dai Ahmad shiru yayi sai yatsun shi daya keta faman murza. murmushi malam Mamuda yayi kamin yace "to tashi kaje zamu yi magana da Maman ka Allah yayi maka albarka ya kuma k'ara tsareka ka jika ko? Allah yaji kan mahaifinka."

Tsabar kunya ta hana shi karasawa cikin gidan ya gaishe da Maman khadija d'in a kunya ce yabar zauren, yayin da malam Mamuda ya bishi da kallon kauna yana murmushi tare da godema Allah da samun siriki kamar Ahmad.(sai kace wani babba)


******

Dafaffar gyad'a ya gani a hanya ya tsaya ya siya sannan ya nufi gidan su yana mejin kunyar ganin khadijan.

Yajima tsaye yana kare mata kallo tun daga yatsun kafarta har zuwa gashin kanta tallabe kumatun shi yayi da hannu d'aya yana tunanin shiko me zaiji ajikin khadija wadda da alama ko kirgen dangima kila bata faraba shida ya kejin bukatar kasan cewa da mace.
 
_Abin da dariya koshi Ahmad d'in nawa yake da har yake raina wani.?_

Saida ya gaji da tsayuwa sannan yayi sallama ya shiga gidan sannun sukai mishi sannu shi kuma kai tsaye ya wuce d'akin Mama da ledar a hannunshi.

Zama yayi tare da furta "washhhhh Allah na....!"
kallon shi tayi kamin tace "sannu daga ina haka?" Yace,

"Mama wajan baba naje munyi magana dashi amma kuma yayi min maganar khadija Mama me zanji ajikin khadija dan Allah haba...?" idasa maganar yayi cike da yarinta da shagwab'a tare da nuna shifa babba yake SO. kauda kanta tayi ga barin kallon shi kamin tace "kayi hakuri da ita itama babu abinda ba zata iyaba indai ka lallab'ata kuma ka bata kulawa, gobe insha Allah zanje tsaranci in gayama dangin babanka."

Gyadar ya juye a kasa ba tare daya kula da maganar data yiba ya faraci itama faraci tayi tare da yin nazarin fuskarshi, Aminu da khadijan ta kwalama kira sai gasu sun shigo tare, Ahmad idanunshi basu tsaya ko inaba sai akan kirjin khadija aiko nan yaga abubuwan arziki sunfara futowa be san lokacin da murmushi ya kwace mishi ba cikin ranshi ya furya ikon Allah ashe ta fara (duk da yarinya ce sai dai tana da garin jiki hakan yasa kirji ya fara tasowa)

Suna cin gyadar suna hira yayin da shi kuma ya kafeta da idanun shi yana kallon duk wani motsi nata ba tare daya san da kallonshi da Maman shi keyi ba. yana d'aga idanun shi suka had'e dana Maman aiko nan da nan ya d'ibi gyadar a hunnshi ya fice yana dariya cike da kunya, shi kanshi be san yadda akai yake irin wad'and'an abubuwan ba.......


    Washe gari; juma'a kenan haka Mama ta shirya cikin zullumi gami da tunanin irin karb'ar da dangin mijin nata za suyi mata sai dai bakinta cike yake da addu'ar samun nasara.

"Kai Aminu idan Allah yasa ka dawo daga makaranta to kaje gidan su khadija ka zauna har in dawo kanaji nako?"

Ihun kuka ya saki kamin ya baje k'asa ya fara kukan shi wallahi sai ya bita.
Ahmad ya fito daga d'akin shi cikin shirin makaranta yace "Mama kije da shi dan Allah tun da yana so na san daga yau idan yaje ba zai kuma marmarin sake zuwaba."

 Tare suka bar gidan inda Ahmad ya rike mukullin gidan a hannunshi ya rakasu har inda za su hau motar Tsaranci sannan ya wuce makaranta shi kuma.


Lafiya lau suka isa gidan ainihin iyayen mijin nata ta, aiko tsohuwar ta  tarbeta da murna da farin ciki nan ta bata ruwa gamida abinci Aminu kawai yaci itako tace Alhamdulillahi.
 
"To habiba lafiya kuwa kike tafe yanzu ba zato ba tsammani?"

 Mama tace "Eh inna lafiya lau wallahi dama nazo wajansu Yaya salisu ne."

"To madalla bari a sakko masallaci duk zaki gansu sun shigo ai gabaki d'ayan su."

Aiko kamar had'in baki bayan sallar juma'a sai gasu sunata shigowa duk wanda ya ganta sai kaga fuskar shi ta canza daga walwala zuwa rashinta. su bakwai ne duk maza kuma magidanta ne gabaki d'ayan su, fulanine sosai sabida cikin suma akwai wa inda har yanzu sukan tab'a kiwo.

Bayan gaishe gaishe da aka gabatar sai ta fara magana a d'add'are "Dama zuwa nayi akan maganar babana."
Alhaji salisu wanda da alama shine babba sabida jikinshi daya nuna hakan, yace "ke mufa ba shashashai bane in zaki gayamana meke tafe dake ki gaya mana in kuma shiru za kiyi saimu watse muna da abin yi."

Wani daga gefe yace "hala kulleshi akayi a prison?" Da sauri ta kalleshi tare da girgiza kai. wani ma yace to "kila shaye-shaye ya fara ko?" zuwa yanzu har idaunta sun fara cika da kwalla sabida yanda take ji suna jifan yaronta da mugun furuci sai kace ba 'ya'yan d'an uwansu ba.
   
Cikin alamun karayar zuciya tace "dama aure yake so shine nace bari nazo nagaya muku."
gaba d'ayan su suka d'auki salati sai kace sunji wani mugun abu ko wanne hannu rike da baki. kamin babban yace "tab ai Hamisu maganarka akan hanya take da kace shaye-shaye yake yo in ba haka ba yama za ayi ace kamar me sunan baba ya san me ake nufi da aure, koda yake wata kila ya dami yaran mutane da yimusu fyade shiyasa uwarshi ta keso ta aurar dashi kamin asirin shi ya tono. To maganar gaskiya wannan magana taki ta ban zace domin ko anan ruga kamar me sunan baba besan komaiba na danga ne da aure ba balle ku da kuke cikin binni, bama wannan ba wane dan iskan uba kike ganin zai d'auki yarinyar shi ya bashi yana a haka yaro jagal sannan babu cas! babu as! to ni dai amatsayi na babba na yanke hukunci babu ruwanmu da sha'anin yaranki sabida haka ki gama hutawa ki kama gaban ki kin daiji abin da nace ko?"

Kowanen su yana tofa albarkacin bakin sa suka bar d'akin sai ya zamana daga sirikar ta sai Aminu wanda ya shige jikin mahaifiyar shi ganin tana kuka.
 
"Kiyi hakuri habiba insha Allah wata rana sai labari ban san me ibrahim yayo ma 'yan uwan shiba da suka kulla ceshi da zuri'arshi alhalin gashi be raye shiko wannan babban kawai nasan dan kinki auran shine shi yasa yake miki wani abun, kije inkina da hali kimi shi auren sabida samun kwanciyar hankalinki ni dai bani da komai habiba dana temaka miki kuma kin dai san yaran nan ba suji magana ba dana tilasta musu kiyi hakuri kinji tashi ki karasa gidan naku."

Tana rike da hannun Aminu ta shiga zauren gidansu zaune ta tadda mahaifinta yana ta jan casbaha.
 zubewa tayi gaban shi tare da sakami shi kuka domin dama habiba irin matan nan ne masu saurin kuka, "ashsha ashsha habiba daga ina haka da kuka?

Cikin kukan take magana "baba daga gidan su marigayi nake."

"To meya kai ki tunda kin san ba sonki suke yi ba shike nan ke kullun sai sun sakaki kuka Allah na gode maka da kaddarar daka jarabci d'iya ta da ita ina fatan ka share hawayenta wataran ka hanata zubar da hawayenta sai akan farin ciki Allah."

Aminu ya jawo jikin shi yana murmushi tare da cewa "kai d'an birni ina yayan ka ne yayan ka ya gujemu ko?"

 A hankali aminu ya gai dashi sannan tsohon ya ci gaba da yi mai tambayoyi cikin wasa. saida yaga ta nutsu tabar kukan sannan ya tambayeta meya faru?

"Baba dama yayan Aminu ne yake bukatar aure shine nazo nagayama iyayen shi maza amma baka ga irin tozar cin da sukai minba."

Murmushi yayi irin nasu na manya kamin yace "gara da Allah ya kawoki domin kiwon da kike yi ma duk na sai dasu sabida yanda naga amfara yi musu d'auki d'aya d'aya sannan hatta gonakin ki biyu suma duk na had'a nakai ma me gari sabida hak kamin ki tafi za muje ki amshi abinki ki ajiye wajanki kin dai san halin ladidi baza tabar miki komai ba tunda tasan nakine ba nawaba."

Cikin nishad'i tace "To baba nagode sosai to amma da kuwa sonake nasai da gonakin duka."

"Aha'ah habiba baza kiyi haka ba kud'in kiyon ki sunada yawa sosai sannan sai ki saida gona d'aya ki had'a kud'in nasan har ragowa sai kinyi ita kuma d'ayar saiki ajiye sabida gaba Allah yayi miki albarka ya kuma albarkaci yaranki wataran sai labari habibi insha Allah wataran zaki yi dariya koda bayan raina ne zaki tuna maganata kinji ko kije ki gaida ladidin sai kizo muje wajan megarin a karb'o."

Mik'ewa tayi tashiga gurin tayi sallama tayi kusan goma sannan tafito kallon banza tayi mata kamin tace "nifa ban san ina barci atasheni lafiya?" Duk'awa habibi tayi tare da gaisheta sai dai ko kallon banza bata samu ba ta gaji da durkushenta ta fita wajan babanta tana sharar kwalla.


A kalla ta baro Tsaranci da kud'i masu tarin yawa domin dama inda Allah ya rufamata asiri kenan tana da kadarori. sai da magriba ta shiga gida a gajiye take sosai. Zaune ta tadda Ahmad ya zabga tagumi cike yake da zullumin yanda Maman zata dawo. Ruwan wanka yakai mata tare da ajiye na alwala gefe hankalin shi ya kwanta ganin yanda ta dawo da walwala.

Sai da tai sallar i'sha'i sannan taci abincin da Ahmad ya dafa shinkafa da miya hadda salad ya yanka😅tanaci tana murmushi sabida yanda taji dad'in girkin.
a haka ya shigo ya taddata. jakar data shigo da ita ta nunamishi alamar ya d'auko, zama yayi gefenta tare da bud'e jakar, ganin kud'in dake ciki yasa shi mekewa ba tare daya shirya ba cikin tsananin tsoro......

    Cike da tuhuma yake kallonta, wannan dalilin ya sata binshi da kallo tare da cewa "Haba babana zauna mana sabida Allah ka wani tashi tsaye kana zaro min idanuwa..!!"

Ba tare data kuma kallon shi ba tace "kafin ka fara zargina ka tunga tuna cewar ni d'in mahaifiyar kace, gona ta d'aya na sai da d'ubu dari shidda da hamsin sauran kuma na shanaye nane da tumaki da awaki da zabbi da kaji na sune baba ya sai da sabida yanda mutane keta kame su."

A jiyar zuciya ya sauke sannan yace "To mama naga wannan ma na gona ne takar dun?"

"Eh d'ayar gona tace aika san biyune ko?"

"Yanzu kaje ka karamin babanku malam Mamuda kace mai ina son magana dashi."

Maida jakar yayi ya ajiye sannan ya fice bakin shi cike da adduar fatan alkhairi ga iyayen shi musamman uwa masha gwagwar maya komai da ruwanki.


   Gaba d'aya ta kwashe kud'in kiwonta ta boye sai tabar kud'in gonar kad'ai. Tare suka shigo gidan sai dai Ahmad d'akin shi ya wuce. bayan sun gama gaisawa ne ta shai dami shi komai daya faru daga dangin baban Ahmad sannan ta mikamishi kud'in tace na gonarta ne d'aya ta saida. beyi mamakin dajin amsar dangin abokin nashi ba domin yasan su farin sani makuwa, sannan ya dora da cewa "amma dai daba kiyi saurin sai da gonaba sabida nima ina nan ina bakin kokarina, sannan na yanke hukunci ranar juma'a me zuwa za a d'aura musu auren a masallaci sabida nagaya ma liman ma d'azu, in yaso sai a tada musu gini acan wajan dakin shi aimusu d'aki ciki da falo da bayi sai kuma dan tsakar gida ko kamar babbar tabarma ne, tunda Allah yasa wannan gidan yana da girma sosai dole su zauna a gaban ki sabida dole sai da zuba musu idanu sabida yarinta na damun su duka biyun.
 
Cikin farin ciki ta Amsa da "Alhamdulillah malam hakan yayi Allah ya sanya Alkhairi acikin lamarin ya basu zaman lafiya mun gode sosa Allah ya saka da alkhari, yanzu sai ka tafi da kud'in wajan ka idan aka d'ibi na sadaki da sauran kayan aure sai a tadana damusu na ginin."

"Eh hakan yayi amma dai ki ajiye kud'in wajanki tukunna idan Allah ya kaimu gobe zanzo....
Ku biyo don jin yadda zata kasance..

Post a Comment

0 Comments